Yin titin da ya haɗa Dawasa, Kukuri da Chukuriwa zai bunƙasa harkokin kasuwanci a yankin – Mazauna yankin 

0
55
Yin titin da ya haɗa Dawasa, Kukuri da Chukuriwa zai bunƙasa harkokin kasuwanci a yankin

Yin titin da ya haɗa Dawasa, Kukuri da Chukuriwa zai bunƙasa harkokin kasuwanci a yankin – Mazauna yankin 

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mazauna garuruwan Dawasa, Kukuri da Chukuriwa na ƙaramar hukumar Nangere a jihar Yobe sun bayyana cewa gina titin kilomita 16 a tsakanin garuruwan uku, idan aka kammala zai bunƙasa harkokin kasuwanci a yankin.

Al’ummar yankin sun bayyana ra’ayoyinsu ne a ranar Talata a lokacin da ƙungiyar ‘yan jarida ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar ta ƙasa reshen jihar Yobe, Komared Rajab Ismael suka ziyarci al’ummomin yankin a wani rangadin aikin yaɗa labarai.

Da yake zantawa da manema labarai a garin Chukuriwa, Hakimin garin, Alhaji Lawan Mohammed ya yabawa Gwamna Mai Mala Buni kan wannan gagarumin yunƙuri.

“Buni ya yi mana komai musamman wajen gina wannan hanya ta musamman da ta haɗa al’ummarmu da unguwarmu da muka daɗe muna buƙatar ta,” inji Hakimin garin Chukuriwa.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Japan za ta taimaka wa mata da yara sama da dubu 3 a harkar kiwon lafiya a Yobe

A garin Kukuri, Malam Ishaku Adamu, (Masaya Kukuri), ya ce gina titin mai tsawon kilomita 16 zai sauƙaƙa zirga-zirga da kuma bunƙasa ayyukan noma.

Tun da farko tawagar manema labarai sun ziyarci aikin titin Karasuwa da Garinguna mai tsawon kilomita 18 da aka gina a ƙaramar hukumar Karasuwa wanda tuni aka kammala shi da kuma Chumbusko-Tagali, titin mai tsawon kilomita 10 da ake shirin kammalawa a ƙaramar hukumar Bade ta jihar.

Yayin da yake a Tagali, Wakili na al’ummar yankin, Malam Kakdu Kafayo ya yaba wa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni kan aikin hanyar, ya ce titin kilomita 10 da gwamnatin jihar Yobe ta yi ya samo asali ne sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a shekarar 2022 a unguwar, inda Gwamna Buni ya kai ziyarar jaje da tausayawa.

Tawagar ‘yan jarida ta kuma ziyarci hanyar Fika zuwa Maluri mai tsawon kilomita 22.5 a ƙaramar hukumar Fika a jihar.

A wurin aikin Fika-Maluri mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Fika, Ahmed Abubakar ya ce aikin titin na ɗaya daga cikin ayyukan da ɗaukacin al’ummar garin Fika da maluri ke ci gaba da yi, kuma wannan abu ne da gwamnatin yanzu ta bari a baya a cikin jihar.

“Aikin titin Fika-Maluri yana haɗe da garuruwa biyar kuma zai kai mutane zuwa ƙananan hukumomin Gujba da Gulani da ke maƙwabtaka da ƙaramar hukumar.

A nasa jawabin bayan rangadin aikin, shugaban ƙungiyar NUJ na jihar Yobe, Kwamared Rajab Mohammed ya yabawa ƙoƙarin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni na gina dukkan hanyoyin a yankunan da aka ziyarta wanda a cewarsa gwamnan ya kawo ribar dimokuraɗiyya ga jama’ar Yobe.

“Mun ji ta bakin dukkan al’umma da muka zagaya, kuma mun ga matakin da ake gina wa titin a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta hannun kwamishinan ma’aikatar ayyuka, Injiniya Umar Wakili Duddaye, ayyukan ba su da wata matsala, hakan na nufin aikin da ake yi a can yana da kyau kuma yana faranta ran jama’a,” in ji Kwamared Rajab.