Yaƙin Sudan ya haifar da matsananciyar yunwa a yankin Darfur
Wani rahoto da hukumar sa ido kan ƙarancin abinci da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar a jiya Alhamis, ya nuna cewa yaƙin da aka shafe sama da shekara guda ana yi a Sudan ya jefa wasu sassan arewacin Darfur cikin ƙangin yunwa, ciki har da sansanin ‘yan gudun hijira, inda aka tsugunnar da mutane sama da rabin miliyan.
A cewar rahoton, an yi hasashen za a fuskanci bala’in yunwa a karon farko a tarihin binciken shirin da ake ƙira IPC a Sudan.
An kuma ayyana yankuna 14 a matsayin masu fuskantar barazanar bala’in yunwa a cikin watanni masu zuwa, kamar yadda Kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya, Stephane Dujarric ya shaidawa manema labarai, game da mizanin IPC, shirin da ke sa ido kan ƙarancin abinci na duniya.
KU KUMA KARANTA;Kusan mutane miliyan 26 a Sudan na fama da matsananciyar yunwa – MƊD
Mizanin tsarin na IPC bai ayyana bala’in yunwa ba, amma ya ba da hujjojin da za a ayyana bala’in yunwa a hukumance.
Tsarin na IPC ya ce matsalar yunwa ta fi ƙamari a arewacin Darfur, ciki har da sansanin ‘yan gudun hijira na Zamzam, wanda ke tazarar kilomita 12 kudu da El Fasher babban birnin yankin, kuma ta yiwuwa yanayin ya tsananta har zuwa ƙarshen watan Oktoba.