Hukumar Hisbah ta haramta wa ɗaliban Kano bikin kammala karatu

0
69
Hukumar Hisbah ta haramta wa ɗaliban Kano bikin kammala karatu

Hukumar Hisbah ta haramta wa ɗaliban Kano bikin kammala karatu

Hukumar Hisbah ta haramta wa ɗaliban sakandare a Jihar Kano gudanar da bikin kammala karatu da aka fi sani da Candy.

Bisa al’ada dai ɗaliban da suka kammala rubuta jarrabawar fita daga sakandare kan gudanar da shagulgula don nuna farin cikinsu bisa ganin lokacin.

Da yake ganawa da manema labarai, Darakta-Janar na Hukumar Hisbah, Abba Sufi, ya bayyana cewa duba da yadda aka sami korafe-korafe game da yadda irin daliban suke nuna halaye marasa kyau da sunan murna, ya sa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci Hukumar ta ɗauki matakin da ya dace.

A cewar shugaban na Hisbah “Mun damu kwarai game da yadda yaranmu da suka kammala rubuta jarrabawarsu ta sakandare suke tayar da rigingimun a tsakaninsu.

“Wasu suna yayyaga kayan makarantarsu, wasu kuma suna ɓata su da rubuce-rubuce marasa amfani.

KU KUMA KARANTA: Alƙawura 5 da Abba ya yi wa Sheikh Daurawa da ’yan Hisbah

“A gaskiya wannan ba abu ne mai kyau ba.”

Sufi ya ƙara da cewa baya ga wannan kuma dalibai maza suna cudanya tsakaninsu da mata inda suke tafiya wuraren da bai kamata ba duk da sunan murnar kammala makaranta.

“Haka kuma ana samun ɗaliban a wuraren da bai kamata a gan su ba.

“Wannan abu ne da Gwamnati ba za ta zuba ido ta bar shi yana ci gaba da faruwa ba,” in ji shugaban hukumar Hisbah.

Abba Sufi ya yi ƙira ga iyaye da su tsaya tsayin daka wajen sauke nauyin da Allah Ya dora musu na tarbiyyar ’ya’yansu.

Ya yi ƙira ga ɗaliban da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’ar samun nasarar jarrabawar da suka rubuta a maimakon shigar da kansu cikin ayyukan saɓon Allah.

“A matsayinku na ɗalibai kamata ya yi ku mayar da hankali wajen yin addu’a game da samun nasarar jarrabarwa da kuka rubuta.

“Haka kuma a maimakon ku yaga kayan makarantarku kamata ya yi ku ajiye wa kannenku sai su yi amfani da shi,” a cewarsa.

Leave a Reply