An ceto wani jariri da aka kashe mahaifiyarsa a wani mummunan farmaki ta sama a Gaza

0
63
An ceto wani jariri da aka kashe mahaifiyarsa a wani mummunan farmaki ta sama a Gaza

An ceto wani jariri da aka kashe mahaifiyarsa a wani mummunan farmaki ta sama a Gaza

An kashe aƙalla mutane 13 a wasu hare-hare uku da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke tsakiyar Gaza cikin daren Juma’a zuwa jiya Asabar, a cewar jami’an kiwon lafiyar Falasɗinu, yayin da ake ganin ana samun ci gaba a tattaunawar tsagaita buɗe wuta a birnin Alkahira.

Daga cikin waɗanda suka mutu a sansanin ‘yan gudun hijiran Nuseirat da kuma sansanin ‘yan gudun hijiran Bureij, akwai yara uku da mace guda, a cewar ƙungiyoyin agajin gaggawa na Falasɗinawa da suka kai gawarwakin zuwa asibitin Al-Aqsa Martyrs da ke kusa. ‘Yan jaridan AP sun kirga gawarwakin mutane 13 a asibitin.

Mace macen baya-bayan nan na zuwa ne adaidai wani lokaci da ake bege gani a yakin da ya addabi Gaza, bayan da tawagar likitocin suka ceto jariri da rai daga wata mace Bafalasdina mai juna biyu da aka kashe a harin na jirgin sama da ya fada kan gidanta da ke Nuseirat da yammacin ranar Alhamis.

An kashe Ola al-Kurd mai tsohon ciki mai shekaru 25 tare da wasu mutane 6 a tashin bam ɗin, amma jami’an agajin gaggawa suka garzaya da su asibitin Al-Awda da ke arewacin Gaza da fatan ceto yaron da ke cikinta. Sa’o’i kaɗan bayan haka, likitoci sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa an haifi yaron.

Jaririn da har yanzu ba a raɗa masa suna ba yana cikin koshin lafiya, sai dai yana fama da ƙarancin iskar oxygen kuma an sanya shi a cikin na’urar incubator, in ji Dr. Khalil Dajran. Mahaifin yaron ya samu rauni a wannan harin, amma ya tsira da ransa.

KU KUMA KARANTA:Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 48 a Gaza a ƙasa da awa ɗaya

Yakin na Gaza, wanda ya ɓarke sanadiyar hari da Hamas ta kai wa kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 38,900, a cewar ma’aikatar lafiyar yankin, wadda ba ta banbance tsakanin mayaka da fararen hula a kidayar ta.
Yakin ya haifar da bala’in jin kai a yankin Falasɗinawa da ke gabar teku, inda aka raba mafi yawan al’ummarta miliyan 2.3 da muhallansu tare da janyo yunwa mai yawa.

Harin na Hamas a watan Oktoba ya kashe mutane 1,200, galibi fararen hula, sannan mayaƙan sun yi garkuwa da kusan mutane 250.
Kimanin mutane 120 ne suka rage a hannu ake garkuwa da su, inda aka yi imanin kusan kashi uku daga cikinsu sun mutu, a cewar hukumomin Isra’ila.