Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

0
93
Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump - Pennsylvania

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yaƙin neman zaɓen tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.

A cikin sanarwar, Sakataren tsaron cikin gidan na Amurka Mayorkas ya bayyana cewa, “Ni da Daraktan ma’aikatar leƙen asiri Cheatle mun yi wa Shugaba Biden bayani game da harbin da aka yi yau a Pennsylvania. Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) da Ma’aikatar Leƙen Asiri suna aiki tare da abokan aikinmu, masu kula da kiyaye doka don gudanar da bincike kan harbin.

KU KUMA KARANTA:Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna Allah wadai da wannan tashin hankalin da kakkausar murya tare da yaba wa hukumar leƙen asiri bisa matakin gaggawar da ta ɗauka a yau. Muna tare da Shugaba Biden, tsohon Shugaba Trump, da yaƙin neman zaɓensu, kuma muna ɗaukar duk matakin da ya dace don tabbatar da tsaronsu. Kula da tsaron ’yan takarar Shugaban ƙasa da kuma taron yaƙin neman zaɓensu na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da sashenmu ke ba da fifik

Tun farko Mai magana da yawun ma’aikatar leƙen asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leken asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya. Yanzu haka Hukumar tana gudanar da bincike, ta kuma sanar da Hukumar Binciken manyan laifuka ta FBI.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here