Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayani kan yadda aka kashe biliyan N729 na tallafi

0
110
Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayani kan yadda aka kashe biliyan N729 na tallafi

Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayani kan yadda aka kashe biliyan N729 na tallafi

Kotun Tarayyar da ke Legas ta umarci tsohuwar ministar ayyukan jin ƙai a gwamnatin Buhari wato Sadiya Umar-Farouq ta yi bayani kan yadda ta kashe naira biliyan 729 da gwamnatin ƙasar ta bai wa ‘yan Najeriya miliyan 24 a watanni shida na 2021.

Haka kuma kotun ta bayar da umarni ga tsohuwar ministar ta kawo jerin sunayen mutanen da aka biya kuɗin, da kuma jihohin da waɗanda aka biya kuɗin suka fito da kuma adadin da kowace jiha ta samu.

Ƙungiyar nan da ke yaƙi da cin hanci ta SERAP a Najeriya ce ta shigar da tsohuwar ministar ƙara inda ta buƙaci a yi bayani kan yadda aka raba kuɗin a zamanin Buhari.

Kotun ta bayyana cewa ƙungiyar da ta shigar da ƙarar ta buƙaci a ba ta bayanai dangane da kuɗin da aka raba wa ‘yan ƙasar a 2021.

Ƙungiyar ta SERAP ta yi jinjina ga hukuncin da alƙalin kotun Deinde Isaac Dipeolu ya yanke inda ya ce hakan “nasara ce ga gaskiya da riƙon amana wurin kashe kuɗaɗen jama’a.”

Tuni dai SERAP ɗin ta aika wasiƙa ga ofishin shugaban Nijeriya Bola Tinubu da kuma babban lauyan kasar domin su bi umarnin hukuncin da kotun ta yanke.

KU KUMA KARANTA: Shugabannin bankuna na amsa tambayoyi kan badaƙalar Beta Edu da Sadiya — EFCC

“Muna buƙatar ku umarci ma’aikatar jin kai da ta gaggauta tattara tare da fitar da bayanan kashe kudade na naira biliyan 729 (dala miliyan 467) kamar yadda kotu ta bayar da umarni,” in ji mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare a ranar Asabar.

Leave a Reply