Nan da 2030 za a fuskanci matsananciyar yunwa a Nijeriya — Majilisar Ɗinkin Duniya
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewar ‘yan Najeriya miliyan 82, kimanin kashi 64 na ‘yan ƙasar ka iya fuskantar matsalar yunwa nan da shekarar 2030.
Haka kuma MƊD ta yi ƙira da gwamnatin ƙasar ta magance matsalar sauyin yanayi da matsalar ƙwari da sauran abubuwan da yi wa harkar noma barazana.
Jaridun Najeriya sun ambato jami’in Majalisar Ɗinkin Duniyar, Taofiq Braimoh – wanda ya wakilci kodinetan ayyukan jin ƙai na hukumar abinci da ayyukan noma na majalisar na bayyana haka lokacin da yake jawabi kan matsalolin ƙarancin abinci a taron ƙaddamar da shirin bunƙasa ayyukan noma na ‘CropWatch’ a birnin Abuja.
KU KUMA KARANTA:Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi maraba da sakin yara 21 da aka yi garkuwa da su
Mista Braimoh ya ce akwai buƙatar gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan da suka dace cikin gaggawa don magance matsalar.
“Gwamnatin Najeriya tare da haɗin gwiwa masu ruwa da tsaki, sun gudanar da bincike na shekara-shekara da suka saba gudanarwa kan abinci. Sakamakon binciken ya tayar da hankali, kimanin mutum miliyan 82 ne za su fuskanci yunwa nan da 2030,” kamar yadda Jaridun ƙasar suka ambato Braimoh na bayyanawa.
Ya ci gaba da cewa matsalar rashin abinci da ƙasar ke fama da shi, baya rasa nasaba da matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da ita, da matsalar ƙwari da wasu abubuwa da ke yi wa harkar noma barazana a ƙasar.
Hasashen na Majalisar Ɗinkin Duniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsadar abinci, lamarin da ya tilasta wa gidaje da dama haƙura da sayen abincin da suka saba ci.
A cikin rahotonta baya-bayan nan, hukumar ƙididdigar ƙasar ta ce farashin abinci a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 40.66 a watan Mayu, matakin da aka jima ba a ga irinsa ba.