‘Yan bindiga sun kashe mutum 21 a wani bikin aure

0
50
'Yan bindiga sun kashe mutum 21 a wani bikin aure

‘Yan bindiga sun kashe mutum 21 a wani bikin aure

Wata ƙungiya ɗauke da makamai ta kai hari a yayin wani bikin aure a tsakiyar ƙasar Mali tare da kashe aƙalla mutane 21, kamar yadda mazauna yankin suka faɗa a ranar Laraba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin sojojin ƙasar Afirka ta Yamma ke fafutukar yaƙi da tashe-tashen hankula daga masu tsattsauran ra’ayi.

Maharan sun kutsa ƙauyen Djiguibombo akan babura wanda ke garin Bandiagara a yammacin ranar Litinin ɗin da ta gabata yayin da mazauna yankin ke bikin ma’auratan, a cewar Bakary Guindo, shugaban ƙungiyar matasan yankin.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun kashe malamin jami’a a Katsina, sun sace ‘ya’yansa

“Yawancin waɗanda abin ya shafa yankan rago aka musu” in ji Guindo.

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai ya biyo bayan irin wanda ƙungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta JNIM da ke da alaƙa da Al-Qaida ke kai hare-hare a yankin.

Leave a Reply