Shugabannin ƙasashen ƙungiyar AES sahel za su gudanar da taron ƙoli a Yamai

0
96
Shugabannin ƙasashen ƙungiyar AES sahel za su gudanar da taron ƙoli a Yamai

Shugabannin ƙasashen ƙungiyar AES sahel za su gudanar da taron ƙoli a Yamai

 

Shugabanin gwamnatocin mulkin sojan Burkina Faso, Mali da Nijar na shirin gudanar da taronsu na farko a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar AES a ranar Asabar 6 ga watan Yuli a birnin Yamai.

Taron dai na da nufin jaddada haɗin kan da ke tsakanin ƙasashen uku ne bayan da a watan Janairun da ya gabata suka fice daga ƙungiyar ECOWAS.

Waɗannan ƙasashe na fama da aika-aikar kungiyoyin ta’addanci saboda haka babbar maganar kuɗaɗen bai ɗaya taron zai tattauna hanyoyin da za’a tunkari wannan lamari da ke haddasa kisan ɗimbim jami’an tsaro da fararen hula.

KU KUMA KARANTA:ECOWAS na shirin ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya da zai yi aiki a ƙasashen ƙungiyar

Sanarwar fadar shugaban majalissar CNSP na cewa kaftin Ibrahim Traore na Burkina Faso da Kanal Assimi Goita na Mali zasu sauka birnin Yamai da la’asariyar ranar Juma’a a albarkacin taron ƙoli na farko na shugabanin ƙasashen AES da zai gudana a ranar asabar.

Tare da mai masauƙin baƙi Janar Abdourahamane Tiani na Nijar waɗannan shugabanin gwamnatocin mulkin soja za su tattauna akan matsalolin da ke addabar ƙasashen uku.

A watan Fabrairun da ya gabata ne ministoci daga ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso a ƙarshen taron da suka gudanar a Ougadougou suka shawarci shugabanin ƙasashen su yi nasu taron don jaddada abubuwan da suka tsayar mafarin wannan haɗuwa ta Yamai da zai kasance lokaci na saka hannu kan takardun tabbatuwar haɗin kai ta yadda za su kasance masu manufofi guda. Abin da Mahamadou Tchiroma AIssami jigo a ƙungiyar ROTAB ya ƙira ci gaba a ƙoƙarin ‘yantar da yankin Sahel.

Batun kuɗaɗen bai ɗaya na kasashen Sahel na daga cikin abubuwan da waɗannan shugabanni za su tsaida magana a kansu kasancewarsa ɗaya daga cikin igiyoyin da ake zargin Faransa na ci gaba da amfani da su don jan zarenta a wajen kasashen da ta yi wa mulkin mallaka.

Nijar, Mali da Burkina Faso sun faɗa ƙarƙashin mulkin soja sakamakon lalacewar al’amuran tsaro inda ƙungiyoyin ta’addanci ke yaɗa ayyukan da ake zargin ƙasashen yammaci da hannu wajen kitsawa.

Ƙasashen uku dai sun fice daga CEDEAO a watan Janairun 2024 saboda zargin shugabaninta da kaucewa manufofin kungiyar. Sannan sun kafa rundunar haɗin guiwar AES a watan maris ɗin da ya gabata da zummar tunkatar ƙalubalen tsaron da ke haddasa mutuwar sojoji da fararen hula a kowacce daga cikinsu.

Leave a Reply