COPA America: Panama ta yi nasara kan Amurka

0
136
COPA America: Panama ta yi nasara kan Amurka

COPA America: Panama ta yi nasara kan Amurka

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Amurka ta yi Allah wadai da kalaman nuna wariyar launin fata ga ‘yan wasanta a ranar Alhamis, bayan da Panama ta yi nasara a kan Amurka da ci 2-1 a gasar cin kofin Copa America.

A wani saƙo da ta wallafa a shafin X, hukumar ƙwallon ƙafa ta Amurka ta ce “Babu shakka, babu wuri a cikin wasa na irin wannan halayya ta nuna ƙiyayya da wariya.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “Waɗannan ayyukan ba kawai ba za’a amince da su ba ne, amma kuma sun saɓa wa kimar mutuntawa da haɗa kai da muka ɗauka a matsayin hukuma.”

KU KUMA KARANTA:Manchester City ta lashe Firimiyar Ingila sau huɗu a jere

Timothy Weah, wanda baƙar fata ne, yana ɗaya daga cikin ‘yan wasan da aka ci zarafin su. An bai wa ɗan wasan gaba na Amurka jan kati kai tsaye a minti na 18 da fara wasa, saboda hannu da ya sa ya bugi ɗan wasan Panama a bayan kan sa a lokacin da ƙwallon ta fita wajen filin wasa.

Ɗan wasan Amurka Folarin Balogun ya zura ƙwallo a minti na 22 da fara wasan bayan an bai wa Weah jan kati kafin ɗan wasan Panama Blackman ya farke a minti na 26.

Fajardo ya zura ƙwallo da ta bai wa Panama nasara da ci 2-1 a minti na 83.

Weah ya fitar da wata sanarwa ta kafafan sada zumunta, inda ya bayar da haƙuri tare da neman gafarar waɗanda ya ɓata wa rai.

Yanzu haka dai Amurka, wacce ita ce ke karɓar baƙuncin gasar cin kofin na Copa America, muddin tana son zuwa zagaye na gaba to dole ne ta yi nasara a wasanta da Uruguay da zura ƙwallaye wanda ko da Panama ta yi nasara kan Bolivia za ta samu tsallake wa.

Leave a Reply