An tabbatar da mutuwar masu juna biyu a cikin harin da aka kai a Borno

0
124
An tabbatar da mutuwar masu juna biyu a cikin harin da aka kai a Borno

An tabbatar da mutuwar masu juna biyu a cikin harin da aka kai a Borno

An kasha aƙalla mutane 18, yayin da wasu 30 suka jikkata bayan wasu jerin hare-haren da ake zargin wasu mata ‘yan ƙunar baƙin wake ne suka kai a jihar Borno a jiya Asabar, in ji shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta yankin.

Borno dai na cikin shekaru 15 na hare-haren masu iƙirarin kishin Islama wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da humallan su.

Duk da cewa sojojin Najeriya sun rage ƙarfin mayaƙan, amma har yanzu suna kai munanan hare-hare kan fararen hula da kuma wuraren tsaro.

KU KUMA KARANTA:Gobara ta tashi a matatar man Ɗangote

Barkindo Saidu, shine babban Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno, ya ce wasu da ake zargin ‘yan ƙunar baƙin wake ne suka kai hari daban-daban a wajen bikin aure da jana’iza da kuma asibiti, inda suka kashe mutane tare da jikkata wasu da dama a garin Gwoza.

Saidu ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 18, adadin da ya haɗa da ƙananan yara da manya da ma mata masu juna biyu.

Sai dai babu wata ƙungiyar ko wani mutun da ya ɗauki alhakin kai wannan harin.

Boko Haram da ISWAP da ta ɓalle kanta, su ne ƙungiyoyin ‘yan bindiga da suka fi yawan gudanar da ayyukan su a jihar Borno, wani babban yanki na karkara mai girman gaske.

Leave a Reply