Turkiyya ta koro ‘yan Najeriya 103 zuwa gida

0
155
Turkiyya ta koro 'yan Najeriya 103 zuwa gida

Turkiyya ta koro ‘yan Najeriya 103 zuwa gida

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin tarayya ta karɓi ‘yan Najeriya kimanin 103 da aka koro daga ƙasar Turkiyya bisa wasu dalilai da suka shafi baƙin haure da suka haɗa da ƙarewar wa’adin biza da shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, da dai sauransu.

Alhaji Tijjani Ahmed, ƙwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira da baƙin haure ta ƙasa (NCFRMI) ne ya bayyana haka a yammacin ranar Juma’a, a lokacin da ake tantance waɗanda aka koro ɗin a Abuja.

Ahmed, wanda Amb. Catherine Udida, darakta mai kula da al’amuran hijira a hukumar ya wakilta, ya ce hukumar ta yi tsammanin za a aiko mutane 110 amma sai ta karbi 103, dukkansu maza.

“Wasu daga cikinsu sun shafe wasu watanni a sansanin waɗanda aka koro, kuma yanzu da suke nan, muna fatan za mu bi diddigin duk wasu zarge-zargen da aka rubuta a kundin bayanansu.

KU KUMA KARANTA: Ƴan sandan Najeriya sun kama waɗanda ake zargi da satar mutane a titin Abuja-Kaduna

“Za mu bi ta fom ɗin tantancewa, saboda wasu sun ce an kwace fasfo dinsu.

“Za mu bi diddigin hukumomin Turkiyya, saboda har yanzu fasfo mallakin Tarayyar Najeriya ne,” in ji shi.

Leave a Reply