Kotu ta ƙwace dala milyan 4 da dubu 700 da naira miliyan 830 da sauran kadarori daga hannun Emefiele

Kotu ta ƙwace dala milyan 4 da dubu 700 da naira miliyan 830 da sauran kadarori daga hannun Emefiele

Mai Shari’a Yellim Ɓagoro ne ya ba da umarnin a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki, sakamakon buƙatar da lauyan Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa, Bilkisu Buhari, ta gabatar.

Babbar Kotun Tarayya dake Legas ta ba da umarnin wucin gadi na ƙwace fiye da dala miliyan 4 da dubu 700 da naira miliyan 830, da sauran kadarori da dama dake da alaƙa da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele.

Mai Shari’a Yellim Ɓagoro ne ya ba da umarnin a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki, sakamakon buƙatar da lauyan Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa, Bilkisu Buhari, ta gabatar.

KU KUMA KARANTA:CBN ya ba bankuna umarnin saka sabon harajin tura kuɗi

Bayan sauraron lauyan Hukumar EFCC, a hukuncin da ta zartar, Mai Shari’a Yellim Ɓagoro ta ce, “na saurari hujjojin lauyan masu ƙara sa’annan na nazarci buƙatar da aka gabatar tare da takardun dake mara mata baya.

An bayyana cewar kuɗaɗen da za a mayarwa gwamnatin tarayya a matakin wucin gadin na ajiye ne a bankunan “First da Titan da Zenith waɗanda Omoile Anita Joy da kamfanonin “Deep Blue Energy Services Limited da Exactquote Bureau de Change Ltd da Lipam Investment Services Limited da Tatler Services Ltd da Rosajul Global Resources Ltd da kuma Til Communication Nigeria Ltd ke gudanar da su.

EFCC ta doshi kotu ne domin neman ƙwace kuɗaɗen a matakin wucin gadi, ƙarƙashin sashe na 17 na dokar yaƙi da zambar kuɗaɗe ta 14 ta 2006, da sashe 44(2)(b) na kundin tsarin mulkin Najeriya kuma ƙarƙashin hurumin kotun.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *