Kotu ta ba da belin Abba Kyari

Kotu ta ba da belin Abba Kyari

Kotu ta ba da belin Abba Kyari

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin DCP Abba Kyari na tsawon makonni biyu bayan ya shafe watanni 27 yana tsare.

Ana sa ran Abba Kyari zai samu damar yin zaman makokin rasuwar mahaifiyarsa, wadda ta a cikin wannan wata na Mayu.

Mahaifiyar ta rasu ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, 5 ga Mayu, 2024, kuma ta rasu ta bar ‘ya’ya 10 maza biyar da mata biyar, ciki har da Abba, wanda shi ne babban ɗanta.

Yayin da Abba Kyari bai samu damar halartar jana’izar mahaifiyarsa ba, mazauna jihar Borno sun fito da yawa don yi wa Hajiya Yachilla sutura, wacce tuni aka binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada tun a ranar da ta rasu.

KU KUMA KARANTA: A gabana ‘yan sanda suka kashe makiyaya, bayan Abba Kyari ya nemi in ɗorawa Saraki laifin fashi – Ɗan fashi ga Kotu

Kotun ta sanya ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu, domin tantance buƙatar neman belinsa a shari’ar da ake yi kan tuhume-tuhumen da hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta shigar bayan kama shi shekaru biyu da suka gabata a ranar 14 ga Fabrairu, 2022.

A shekarar 2022, hukumar ‘yan sanda ta dakatar da Abba Kyari da wasu manyan jami’an ‘yansanda biyu – Sunday Ubua da James Bawa – waɗanda ake zargi da hannu a cinikin hodar iblis da ta shafi DCP Abba Kyari

Hukumar ‘yansanda ta dakatar da mataimakin kwamishinan ‘yansanda, ACP Sunday Ubua da mataimakin sufeton ‘yansanda, ASP James Bawa daga gudanar da ayyuka da ayyukan ofisoshinsu daga ranar Litinin, 14 ga Fabrairu, 2022,” in ji PSC. wata sanarwa.

Hukumar NDLEA ta kuma bayyana cewa ana neman Kyari bisa zargin alaƙa da ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa.

Femi Babalola, mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, ya yi zargin cewa Kyari da tawagarsa ta Intelligence Response Team (IRT) sun kama wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka shigo ƙasar daga ƙasar Habasha ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 25, amma sun ɗauki hodar mai nauyin 15kg na kayan da aka kama.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *