Masar ta musanta janyewa daga shirinta na shiga shari’ar Kotun Duniya da Isra’ila
Masar ta musanta labaran da ke yawo waɗanda ke cewa ta janye shirin da take da shi na shiga shari’ar kisan ƙare dangi da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra’ila a kotun ƙasa da ƙasa ta ICJ.
Kafar watsa labarai ta Al Qahera ta ruwaito wani babban jami’in gwamnatin ƙasar na cewa rahotannin da ke yawo kan batun ƙasar ta janye aniyarta ta shiga shari’ar labari ne maras tushe.
Majiyar ta tabbatar da cewa “a shirye Masar take domin ta ɗauki duk wasu matakai domin watsi da ayyukan Isra’ila a gaban Kotun Duniya,” inda majiyar ba ta bayar da cikakkun bayanai kan matakan da Masar ɗin ke shirin ɗauka ba.
KU KUMA KARANTA: Kotun duniya ta ICJ ta yi watsi da buƙatar hana Jamus fitar da makamai zuwa Isra’ila
A makon da ya gabata ne Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta bayyana aniyarta ta shiga shari’ar da Afirka ta Kudu ke yi da Isra’ilar a gaban kotun ta ICJ.
Matsayar Majalisar Ɗinkin Duniya
Ma’aikatar ta jaddada cewa ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon tsanani da kuma girman hare-haren da Isra’ila ke kai wa fararen hula Falasɗinawa a zirin Gaza.
Isra’ila ta ci gaba da kai munanan hare-hare a zirin Gaza duk da wani kuduri na kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a yankin.
Kimanin Falasɗinawa 35,400 ne aka kashe tun daga lokacin, yawancinsu mata da kananan yara ne, yayin da wasu kusan 79,400 suka jikkata tun a watan Oktoban bara bayan wani harin da kungiyar Hamas ta kai.
Fiye da watanni bakwai a cikin yakin na Isra’ila, wurare da dama a Gaza sun zama kango inda akasarin jama’ar ke gudun hijira inda suke fama da yunwa da rashin muhalli mai tsafta da magunguna.
Ana zargin Isra’ila da “kisan kare dangi” a kotun ICJ, wadda ta umarci Tel Aviv da ta tabbatar da cewa dakarunta ba su aikata kisan kiyashi ba, da kuma daukar matakan tabbatar da cewa an ba da taimakon jin kai ga fararen hula a Gaza.