Barau Jibrin, Ndume da wasu sanatoci 38 na iya rasa kujerun su 

0
80

Barau Jibrin, Ndume da wasu sanatoci 38 na iya rasa kujerun su 

Rahotannin daga Majalisar dattijan Najeriya na bayyana cewa Sanatoci aƙalla 40 ne ka iya rasa kujerunsu, saboda kasancewar su mambobi a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar ECOWAS ta Afrika ta Yamma, kuma duk suke karɓar alawus-alawus daga majalisun biyu, abin da ya karya doka.

Wasu daga cikin waɗanda tsigewar ka iya shafa sun haɗa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda a yanzu haka shi ne Kakakin Majalisar ECOWAS na Riƙon, Ali Ndume, Abiodun Olujimi, Smart Adeyemi, Tolu Odebiyi da Mshelia Haruna, da kuma wasu da dama.

Lamarin ya taso ne daga wata ƙara da ƙungiyar Bin Diddigin ‘Yan Majalisa (ALDRAP) ta shigar a gaban Babbar Kotun Najeriya, Abuja, inda ƙungiyar ta maka ‘yan majalisar kotu.

ALDRAP dai tun kafin ta je kotu, sai da ta fara yin kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio cewa ya ayyana kujerun sanatocin cewa ba su ne a kai ba, an tsige su, saboda sun shiga wata majalisa sun haɗa mamba ɗin majalisa biyu, wato ta Najeriya da ta ECOWAS, kuma duk ana biyan su a majalisun biyu.

Yayin da suka ga Akpabio bai yi komai ba, sai ALDRAP ta aika masa da takardar gargaɗi, cewa za su ɗauki matakin shari’a.

A cikin wasiƙar da suka aika a ranar 8 ga Afrilu, mai ɗauke da sa hannun Sakataren ALDRAP, Tonye Clinton Jaja, ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa, “Idan Majalisa ba ta ɗauki mataki a cikin kwanaki bakwai ba, to za ta garzaya kotu.

Sun jaddada cewa dokar Najeriya Sashe na 68(1) na Kundin Dokokin 1999, ya haramta wa sanata ya zama mamba na Majalisar ECOWAS.

Kuma ita ma Dokar 2017 ta ECOWAS ta Sashe na 18 ya yi hani da zama mamba a majalisa biyu.

Sun ce ita ma ECOWAS ta haramta ɗan majalisa ya zama mamba a wuri biyu, kamar yadda ta haramta masa karɓar alawus-alawus a majalisa biyu.

KU KUMA KARANTA: Masana sun yi ƙira da a yi sabbin sauye-sauye ECOWAS

ALDRAP ta roƙi babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta jaddada dokar shiga Majalisar ECOWAS, wato inda doka ta ce, duk mai sha’awar zama mamba a Majalisar ECOWAS ko ta Afirka, to tilas sai ya fara yin murabus, ya sauka daga kujerar sa a Majalisar Dattawa.

Sun kuma roƙi kotu ta dakatar da biyan sanatocin su 40 dukkan albashin su da alawus-alawus ɗin da Majalisar Dattawa ke biyan su, saboda kwanan nan aka ƙaddamar da su mambobin ECOWAS, wasu kuma mambobin Majalisar Afrika.”

ALDRAP ta kuma roƙi kotu ta bai wa INEC umarnin shirya zaɓukan cike-gurbi a yankunan sanatocin su 40, domin a zaɓi waɗanda za su maye gurbin su a Majalisar Dattawa, a cikin kwanaki 30.

A ranar 4 ga Afrilu ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da Majalisar ECOWAS ta Shida, bayan cikar wa’adin ta Biyar a ranar 8 ga Maris, 2024.

Leave a Reply