Ministocin Tinubu ne suka sa ba a ganin ƙoƙarinsa – Sanata Jimoh

0
51

Yawancin ministocin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa ba sa ƙoƙari a cewar Jimoh Ibrahim, Sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu a jam’iyyar APC.

Ibrahim ya kuma ce wasu daga cikin ministocin akwai zargin cin hanci da rashawa a tare da su, yayin da wasu kuma ba sa tabuka komai.

Sanatan ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels.

A cewar ɗan majalisar tarayyar, Tinubu yana da tsarin “mafi kyau” da zai tafiyar da mulkin ƙasar, amma babu wani tsari da mataimaka da za su sa ga kai gaci.

KU KUMA KARANTA:Manyan Sanatoci sun kai wa Tinubu ziyara bayan dakatar da Sanata Ningi

Ya shawarci shugaban ƙasar da ya rusa majalisar ministocin sa saboda rashin cancanta.

“Dole ne ka rusa majalisar ministocinka ka naɗa mutane masu ilimi. Majalisar ministoci ta yi sanyi da yawa kuma ba a gani ƙoƙarin gwamnatin ka,” inji Ibrahim.

“Ya kamata ka sallami waɗanda ake zargi da cin hanci da rashawa nan take. Idan ka kasa yin haka, to kai za a riƙa ganin laifi kuma hakan zai zama illa ga ƙasarmu. Ba na nagin yawancin ministocin a matakin farko na A ba. Yawancin su suna cikin makin B ko C.

Leave a Reply