An kama ɓarawon wayan da ya caka wa budurwa wuƙa a Yobe

0
114

Ɓarawon da ya caka wa wata budurwa wuƙa ya ƙwace wayarta a garin Damaturu na Jihar Yobe ya faɗa komar ’yan sanda.

A kwanakin baya ne dai wani ɓarawon waya ya ƙwace wayar budurwar bayan da ya caka mata wuƙa a gadan baya a unguwar Malari a garin Damaturu.

Sakamakon haka aka garzaya da ita babban Asibitin koyarwa na jihar inda a halin yanzu take samun kulawa.

A wata sanarwa, kakakin ’yan sandan jihar ta Yobe, ASP AbdulKareem Dungus ya ce jami’an su sun kama matashin.

KU KUMA KARANTA: Masu ƙwacen waya sun caka wa wata matashiya wuƙa a Damaturu

A cewarsa, wayar da ɓarawon ya ƙwace samfurin Itel ce haɗe da da layi a ciki.

Dungus ya ce za a ci gaba da bincike daga bisani a tura matashin zuwa kotu don fuskantar hukuncin da ya ya daidai da laifinsa, domin hakan zama izina ga na baya.

Leave a Reply