Cutar sanƙarau ta kashe mutum 85 a Yobe

0
497

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin jihar Yobe ta ce cutar sanƙarau ta kashe mutum 85 tsakanin Janairu da Afrilu sakamakon ɓarkewar cutar a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a birnin Damaturu.

Ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke cewa cutar ta yi ajalin sama da yara 200 cikin mako biyu inda ya ce haƙiƙanin adadin shi ne 85.

Ya kuma ce fiye da marasa lafiya 2,510 da suka kamu da cutar a jihar sun samu sauƙi kuma an sallame su daga asibiti.

KU KUMA KARANTA: Gwamnati ta musanta mutuwar mutum 200 sanadiyar baƙuwar cuta a Yobe

Dakta Gana ya kuma ce an tura jami’an lafiya na sa kai sama da 200 zuwa sassan ƙananan hukumomin Potiskum da Fika a wani ɓangare na ƙoƙarin da ma’aikatar take na daƙile cutar.

Ya ce ma’aikatan lafiya sun bi gida-gida domin ganowa tare da tura mutanen da ke da cutar asibiti.

Yankunan arewacin Najeriya na fama da matsanancin zafi a tsukin nan, yanayin da ke haddasa cutar ta sanƙarau.

Leave a Reply