Majalisar Dattawan Amurka ta ba da tallafin dala biliyan 26.6 ga Isra’ila

0
107

Majalisar Dattawan Amurka ta amince a bai wa Isra’ila tallafin soji har na dala biliyan 26.6, ga ƙawar tata da ake zargi da yi wa Falasɗinawan da ke Gaza kisan ƙare-dangi ta hanyar amfani da makaman Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alƙawarin sanya hannu cikin sauri kan ƙudurin na dala biliyan 61 – wanda ya haɗa da tallafi ga Ukraine da Taiwan – bayan da Majalisar ta ba da amincewarta ta karshe, yana mai cewa za a fara isar da tallafin da ake buƙata a wannan makon.

KU KUMA KARANTA: Amurka ta gargaɗi Isra’ila kan shirin kai wa Iran hari

Amurka ta bayyana goyon bayanta ga Isra’ila tun farkon yaƙin a watan Oktoban bara. Amurka ba ta taɓa ja da baya ba wajen bai wa Isra’ila makamai, ba tare da la’akari da asarar rayukan fararen hula da ake yi a Gaza ba.

Amurka tana bai wa Isra’ila dala biliyan 3.8 a matsayin tallafin soji na shekara-shekara kuma galibi tana bai wa ƙawayenta garkuwa a Majalisar Dinkin Duniya.

Leave a Reply