Ta’addanci babbar masifa ce da aka shigo da ita Afirka daga waje – Shugaba Tinubu

0
197

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce ta’addanci “babbar masifa ce da aka shigo da ita” kuma ya zama wata annoba ga nahiyar Afirka.

A jawabin da ya gabatar a wajen buɗe wani babban taron yaƙi da ta’addanci na kasashen Afrika na kwanaki biyu a Abuja babban birnin ƙasar, Tinubu ya bayyana cewa ana kashe biliyoyin kuɗaɗe da suka kamata a yi amfani da su wajen kula da lafiya da ilimi da samar da ababen more rayuwa a nahiyar a duk shekara, duk a wajen sayen makaman yaƙi da ‘yan ta’adda.

“Dole ne mu yi magana a kan wannan mummunan bala’i da aka shigo da shi wanda yake son karya mu, mu ga cewa lallai ba mu bari hakan ya faru ba,” in ji shi.

Ya ce, ‘yan ta’adda na neman ƙarfafa son zuciya a nahiyar da kuma kawar da mulkin dimokuraɗiyya da kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da harkokin tattalin arziki na ƙasashe da dama.

Ya bukaci shugabannin ƙasashen Afirka da su magance talauci da inganta ilimi ba ya ga salon yaƙi da ta’addanci da sojoji ke yi.

Shugaban na Najeriya ya kuma buƙaci takwarorinsa na yankin da su mayar da hankali kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da ake amfani da su wajen samun kuɗaɗen ta’addanci.

“Wadɗanda suke tunanin hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ba ta da wata alaƙa da tallafa wa ta’addanci to sun yi kuskure sosai. Ƙasashen duniya suna da alhakin halin taimakawa a wannan harka saboda da kudaden waje ake hada-hadar ba kudin Afirka ba, wadanda su ke haifar da wadannan miyagun ayyuka,” ya ce.

Mataimakin Sakatare Janar na ofishin yaki da ta’addanci na Majalisar Dinkin Duniya Vladimir Voronkov, ya ce taron na da nufin magance matsalar ta’addanci da ke ƙara ƙamari a nahiyar.

Ya ce ƙungiyoyin ‘yan ta’adda irinsu Daesh/ISIS da Al-Qaida da masu alaƙa da su suna matsawa kudu zuwa mashigin tekun Guinea da ke kudanci da tsakiyar Afirka bayan sun kafu a yankin Sahel, inda ya yi ƙira da a ƙara ba da haɗin kai tsakanin shugabannin nahiyar domin dakile yaduwar ta’addanci.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya buƙaci ‘yan Najeriya su haɗa kansu don ciyar da ƙasar gaba

Shawarwarin Tinubu

Shugaban na Najeriya ya bayar da muhimman shawarwari a wajen taron ƙolin na yaƙi da ta’addanci na ƙasashen Afrika, kamar:

  1. Samar da wata cibiya ta tsakiya ga kasashen Afirka don musayar bayanai da hada kai don yaki da ta’addanci
  2. Magance tushen ta’addanci, tare da talauci da rashin daidaito
  3. Yanke hanyoyin samar da kudade don ta’addanci, kamar haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma biyan kuɗin fansa
  4. Haɓaka ƙarfi da ingancin ƙungiyoyin da ke yaƙi da ta’addanci
  5. Ƙirƙirar dakaru na musamman don mayar da martani cikin gaggawa game da ta’addanci da sauran barazanar tsaro
  6. Kafa kwamitin da zai haɗa kai da samar da jagoranci kan yaki da ta’addanci
  7. Ƙarfafa ƙarfin yaƙi da ta’addanci na daidaikun ƙasashe
  8. Dakatar da yaɗuwar makamai masu haɗari a faɗin Afirka.
  9. A dauki kwakkwaran mataki don magance barazanar tsaro a nahiyar.

Taron mai taken karfafa haɗin gwiwa tsakanin shiyya da kafa cibiyoyin yaki da ta’addanci a nahiyar Afirka, ya samu halartar mataimakiyar babban sakataren MƊD Amina Mohammed da shugabannin ƙasashe da gwamnatocin ƙasashen Afirka da dama da kuma manyan jami’an MƊD.

Leave a Reply