‘Gwamna Dauda bai ciwo bashin kuɗi ba’

0
168

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda ta bayyana cewa rancen kuɗi biliyan 14.26 , wani ɓangare na kuɗaɗen da gwamnatin da ta shuɗe ta ciwo ne Naira biliyan 20. Amma hawan gwamna Dauda Lawal bai ciyo bashin ko sisin kwabo ba .

Mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfaran a ɓangaren yaɗa labarai, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana haka a takardar da ya sanya ma hannun ga manema labarai.

“Muna so mu fayyace rahoton ofishin kula da basussuka (DMO) cewa gwamnatin jihar Zamfara da ta shuɗe ne ta ciyo bashin Naira biliyan 14.26.

“Gwamnatin jihar Zamfara ba ta taɓa neman rance ko tuntuɓar majalisar jiha ko ta ƙasa domin neman wannan buƙata ba.

“Ya kamata a lura da kyau cewa gwamnatin jihar Zamfara da ta shuɗe ta yi amafani da naira biliyan 20.

KU KUMA KARANTA: El-Rufai ya bar wa jihar Kaduna ɗimbim bashi – Gwamnan Uba Sani

“Gwamnatin da ta shuɗe ta karɓi Naira biliyan 4 daga cikin rancen biliyan 20 da aka nema domin aikin filin jirgin sama na Zamfara, duk da cewa ba a yi amfani da kudaden ba.wajan aiki ba.

“Bayan da muka hau gwamnati, mun gano cewa sharuɗɗan biyan kuɗin ya sa kawo ƙarshen yarjejeniyar ba zai yiwu ba, ba tare da jawo babbar asara ga jihar ba.

“Ma’auni na Naira biliyan 16 daga cikin Naira biliyan 20 da gwamnatin da ta shuɗe ta karɓo shi ne Naira biliyan 14.26 da ofishin kula da basussuka (DMO) ya kama. An rage darajar saboda hauhawar farashin kaya.

“Ba a yi amfani da ma’auni na rance, wanda har yanzu yana cikin asusun gwamnati, kuma za a keɓe shi ne don aikin filin jirgin.”

Leave a Reply