Fulani sun koka akan yadda ake cin mutuncinsu a shafukan sada zumunta

0
114

Daga Ibraheem El-Tafseer

A Najeriya, wata ƙungiyar dattawan Fulani ta duniya mai suna ”Tabital Pulaku International”, ta bayyana damuwa tare da Allah-wadai, da yadda ake amfani da shafukan sada zumunta ana yi wa al’ummar Fulani kuɗin goro wajen aibata su da cin zarafinsu da kuma ɗaukar duk wani Bafulatani a matsayin mai aikata miyagun laifuka.

Ƙungiyar ta ce bai kamata hukumomi su zura ido suna kallo ana muzanta al’umma guda, sakamakon wasu bara-gurbi ‘yan ƙalilan da ke cikinta ba.

Ƙungiyar ta ce a yanzu an mayar da shafukan sada zumunta, wani dandali da ake yi wa al’ummar Fulani da shugabanninsu dukan ɗiyan kanya, ana zaginsu da cin mutuncinsu da yaɓa masu duk wasu baƙaƙen maganganu.

KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar Fulani sun yi taron dawo da darajarsu

Awwal Gonga, mataimakin shugaban reshen ƙungiyar a Najeriya, ya ce ana yin zage-zage da cin mutuncin Fulani a shafukan sada zumunta, amman kowa ya yi shiru a Najeriya, “a duniya ba a danganta laifi da ƙabilanci ko addini. “

Awwal Gonga ya ce Fulani ƙalilan ne ake samu da aikata laifi saboda haka bai kamata ana ma Fulani kuɗin goro ba, ‘kada a danganta laifin mutum da ƙabilarsa kuma gwamnati ta yi aikinta.”

Gonga ya ce masu aikata miyagun laifukan nan, duk da ƙanƙantar yawansu a cikin al’ummar ta Fulani, tamfar cinnaku ne. Domin kuwa ba su san na gida ba, hatta su ma Fulani makiyayan ba su tsira daga hare-haren ‘yan bindigar ba.

Duk da yake dai kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba kowanne ɗan ƙasa damar faɗar albarkacin bakinsa, amma Awwal Gonga na ƙungiyar dattawan Fulanin ta duniya, yana ganin akwai buƙatar baki ya san abin da zai faɗa, don kada garin neman lada a riƙa ture kurtun alhaki.

Leave a Reply