Wata kotu a Sifaniya ta ba da belin tsohon ɗan ƙwallon ƙafar Brazil da kuma Barcelona, Dani Alves, kan dala miliyan 1.1.
Sauran sharuɗɗan belin sun haɗa da cewa Alves zai ajiye fasfo ɗinsa na Brazili da na Sifaniya, domin gudun ka da ya fice daga Sifaniyar.
A ranar Laraba ne wata kotun Barcelona ta ce za a iya sakin Dani Alves daga gidan yari kan belin dala miliyan 1.1, yayin da yake aukaka ara kan shari’ar da ake masa kan aikata fyaɗe, bayan ya yi zaman kusan kwatan wa’adin shekaru huɗu na hukunci.
Haka nan kuma, kotun ta ɗora masa dokar hana Alves zuwa kusa da wadda ya aikata laifin kanta, da tazarar mita 1,000.
KU KUMA KARANTA: Ana yi wa yara fyaɗe sakamakon yaƙin da ke faruwa a Sudan – MƊD
An tsare tsohon ɗan wasan baya na Barcelona da Juventus da PSG a wani gidan yari na Barcelona tun watan Janairun 2023.
An yanke wa Alves hukunci ranar 22 ga Fabrairu, kan laifin yi wata mata fyaɗe a banɗaki wani gidan rawa na Barcelona a 2022, kuma aka umarce shi ya biya ta Euro dubu 150,000.
Sai dai ya ɗaukaka ƙara kan hukunci, kasancewar hukuncin ba shi ne na ƙarshe ba.