Kotu ta haramta wa miji magana da matarsa na tsawon mako 2

0
310

Wata Kotu Majistare a Ado Ekiti fadar Jihar Ekiti ta haramta wa wani mutum yin magana da matarsa na tsawon mako biyu har sai sun sake dawowa kotun ranar da za ta sake zama.

Babban Majistare Dolamu Babalogbon ne ya bayar da umarnin ga mijin matar mai suna Chibuke Nwakedi mai shekara 43 inda ya haramta masa yi mata magana baka-da-baka ko ta waya sai dai ta hanyar wani a tsakani ko kuma ta hanyar magana da lauyanta.

A yayin gabatar da ƙarar mai gabatar da ƙara Sufeton ’Yan sanda Sodik Adeniyi ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara a ranar 3 ga watan Maris ɗin nan da misalin ƙarfe 8:00 na dare ya daki matarsa mai suna Blessing Nwokedi inda ya buga kafarta da gadon katako wanda hakan ya jawo mata targaɗe.

KU KUMA KARANTA: Ta zuba wa mijinta ruwan zafi saboda ta ƙi zuwa biki da ita

Wanda ake ƙarar kuma a wannan lokaci ya yi ƙoƙarin tayar da husuma wanda haka na iya kaiwa ga tashin hankali kuma hakan ya saɓa wa doka da za a iya hukunta shi a bisa tanadin sassa na 186 da 181 na Kundin Manyan Laifuffuka na jihar na shekara 2021.

Lauyan wanda ake ƙara Barista Gbenga Aribiyi na roƙi kotun ta bayar belin wanda ake ƙara yana mai alƙawarin ba zai gudu ba kuma zai gabatar da masu tsaya masa nagartattu.

Alkalin kotu daga ƙarshe ya bayar da belinsa a kan Naira 50,000 da tare da kawo masu tsaya masa mutum biyu da za su ajiye wannan kuɗi sannan ya ɗaga ci-gaba da sauraron ƙarar zuwa 28 ga wannan wata.

Leave a Reply