Najeriya ta samu tallafin dala biliyan 1.3 Don ƙarasa hanyar jirgin ƙasa daga Kano zuwa Nijar

Najeriya ta samo tallafin dala biliyan 1.3 domin kammala aikin layin dogo da zai haɗa Kano, birni mafi girma a arewacin Najeriya zuwa Maraɗi dake maƙwabciyar ƙasar Nijar, in ji ma’aikatar sufuri a ranar Laraba.
Ana sa ran layin dogon zai ƙarfafa tattalin arziƙi da zamantakewar da ke tsakanin ƙasashen domin bunƙasa hulɗar kasuwanci da al’adu tsakaninsu.

Sanarwar da ma’aikatar sufuri ta fitar ta ce, za a ba da tallafin ne daga wata gamayyar haɗin gwiwa da kamfanin gine-ginen na ƙasar Sin (CCECC) ke jagoranta, wanda zai ba da kaso 85% na jimillar kuɗaɗen.

Gwamanatin Najeriya kuma za ta biya sauran kaso 15% tare da bankin fitar da shigar da kaya na Afirka da kuma bankin raya ƙasashen nahiyar Afirka.

Kakakin ma’aikatar sufuri Jamilu Ja’afaru ya ce “samun dalar Amurka biliyan 1.3 na nuni da wani gagarumin ci gaba wajen kammala wannan muhimman ababen more rayuwa.”

KU KUMA KARANTA:Kotu ta ƙi amincewa a saki bayanan kadarorin Buhari da Jonathan

A watan Yuli, kamfanin gine-gine mafi girma a ƙasar Portugal Mota-Engil ya tattaɓa hannu kan wata kwangilar Euro miliyan 840 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 919 don samarwa da kuma ba da kuɗin jigilar layin dogon.

Gwamnatin Najeriya ta yi ƙoƙarin sake gina arewacin ƙasar da ke fama da talauci, wanda wasu sassa na ƙasar suka yi ɓarna tun shekaru goma da suka gabata a hannun masu kaifin kishin Islama.

Wannan aiki dai wani shiri ne na gina layin dogo a faɗin Najeriya domin magance rashin wadatattun ababen more rayuwa da ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arziƙin ƙasar shekaru da dama.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *