Tsananin Zafi: Mai azumi na buƙatar ruwa sosai a jikinsa — Masana

0
153

Masana a Najeriya sun gargaɗi masu azumtar watan Ramadan a wannan shekarar kan su yawaita shan ruwa, sakamakon tsananin zafin da ake fama da shi da ka iya haifar da cututtuka sakamakon rashin wadataccen ruwa a jiki, musamman ga masu aikin ƙarfi ko wahala a wuraren da zafin rana ya yi yawa.

A wata sanarwa da Hukumar kula da bayar da rahotannin yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar a shafinta na X a watan Fabrairu, ta yi hasashen cewa yankin arewa zai fuskanci tsananin zafin da ya kai maki sama 41 a ma’aunin salshiyas, sannan sama da maki 39 a yankin kudancin ƙasar.

Azumin bana ya riski al’ummar Musulmai a jihohin Najeriya a irinsu Kano da Sokoto da Zamfara da babban birnin tarayya cikin tsananin zafi, kuma tuni likitoci irin su Dakta Muhammad Dauda Haroon na asibitin koyarwa na ATBU da ke jihar Bauchi, ya ce an fara kai musu marasa lafiya da tsananin zafin ya yi wa illa, waɗanda kuma sun ɗauki azumi a bakinsu.

KU KUMA KARANTA: Yadda azumin Ramadan ke taimakawa wajen tunatarwa da ƙara kusanci da Allah da kuma iyali

”Irin wannan yanayin ya fi ƙamari kan masu aikin ƙarfi, ko waɗanda suke gudanar da sana’o’insu cikin yanayin tsananin rana,” in ji Dakta Muhammad Dauda Haroon.

Likitan ya ƙara da cewa ”Idan ruwa ya yi ƙasa a jikin ɗan’adam zai dinga jin bakinsa yana yawan bushewa, sannan yawan fitsarinsa zai ragu ya kuma yi duhu, hakan na iya haifar da matsalolin rashin ƙarfin jiki da ciwon kai da tashin zuciya da amai da dai sauransu”, kamar yadda ya shaida wa TRT Afirka Hausa.

Da yake magana da TRT Afrika, Sheik Muhammad Bin Uthman, wani malamin addinin Musulunci da ke birnin Kano na arewacin Nijeriya, ya shawarci Musulmai su sha ruwa sosai a lokacin yin sahur da buda-baki.

Ya ce “Wannan zai rage musu tsananin ƙishi ruwan da ka iya shafar walwalarsu a yayin da suke azumi a tsananin zafi”.

Ya ƙara da cewa, “A yanayi na matuƙar taƙura, ya halatta Musulmi ya karya azuminsa idan azumin zai iya zamowa haɗari ga lafiya ko rayuka, musamman idan karya azumin shi ne kaɗai mafita a gare shi”.

Dakta Muhammad ya bayyana cewa akwai yiwuwar ɓarkewar cututtuka masu alaƙa da zafi da kuma ƙarancin ruwa a jikin ɗan’adam wadanda suka haɗa da cutar sanƙarau da ƙyanda har da suma a wasu lokutan.

Leave a Reply