Daga Ibraheem El-Tafseer
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki a jihar da sa’o’i biyu ga ma’aikatan gwamnatin jihar a cikin watan Ramadan.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri.
Sanarwar ta ce a yanzu ma’aikatan za su fara aiki da ƙarfe 9 na safe kuma za su kammala da ƙarfe 3 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis saɓanin ƙarfe 5 na yamma da aka saba rufewa.
A ranar Juma’a kuma, ma’aikata za su fara da ƙarfe 9 na safe kuma za su rufe da ƙarfe 1 na rana kamar yadda aka tsara.
KU KUMA KARANTA: Yadda azumin Ramadan ke taimakawa wajen tunatarwa da ƙara kusanci da Allah da kuma iyali
Sanarwar ta kuma ce hakan na da nufin bai wa ma’aikatan gwamnati isasshen lokaci don yin shirin buɗe baki na azumi tare da ba da damar haɓaka ayyukan ibada a cikin wannan wata mai alfarma.
Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, “ana fatan ma’aikatan jihar za su yi amfani da lokacin azumin watan Ramadan wajen yi wa jihar addu’ar zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin jihar da ma Najeriya baki ɗaya”.