Jihohi Arewa maso yammacin Najeriya sun yi taro kan sauyin yanayi

0
66

A ci gaba da ɗaukar mataki da ɗan’adam ke yi kan sauyin yanayi da illolinsa, wata ƙungiya, da haɗin gwiwar jihohin arewa maso yammacin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki, sun haɗu a birnin Kano, don neman mafita ta bai ɗaya.

Batun ɗaukar matakai na bai ɗaya wajen magance matsalolin kwararowar hamada da ƙalubalen muhalli da kiwon lafiya sakamakon sauyin yanayi na cikin ƙudurorin da aka cimma a ƙarshen taron kwamishinonin muhalli da sauyin yanayi na jihohin arewa maso yammacin Najeriya wanda ya wakana a Kano.

Baya ga kwamishinonin kula da al’amuran muhalli da sauyin yanayi daga jihohi 7 na shiyyar arewa maso yamma, taron, wanda ƙungiyar raya muhalli ta surge Africa ta shirya, ya ƙunshi shugabannin kwamitocin majalisun dokoki na waɗannan jihohi masu kula da wannan fanni da sauran masu ruwa da tsaki.

Madam Nasreen Al-Amin daraktar ƙungiyar surge Africa tace “Wannan zance da a ke yi akan sauyin yanayi da kwararowar Hamada muna so a ce ya wuce ƙungiyoyin da ba na gamnati ba ne kawai suke magana akai, muna so a kawo wakilan gwamnati, da sune suke yin doka kuma suke aiwatar da ita”.

KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar lauyoyi ta bayyana damuwa kan tauye ‘yancin ba da kariya

A cewar Mahmud Muhammad Abdullahi, guda cikin mahalarta taron kuma kwamishinan raya muhalli na jihar Zamfara, ƙalubalen tsaro da jihar ke fama dashi baya rasa alaka da sauyin yanayi da barazanar kwararowar hamada.

Bakin mahalarta taron dai ya zo wuri guda wajen ganin cewa, ya kamata waɗannan jihohi guda 7 na arewa maso yammacin Najeriya su samar da manufa guda ta yaƙar ƙalubalen da sauyin yanayi ya zo dashi duk kuwa da ‘yan bambamce-bambamcen da ba’a rasa ba a tsakanin su.

Dakta Nura Ibrahim Kazaure shi ne kwamishinan Muhalli na jihar Jigawa, “Ya kamata a ce ko Kano tana yin wani abu na hana sare-saren bishiya ya zama cewa, Jigawa da Kaduna da sauran jihohi sunayi, domin tsarin ya tafi bai ɗaya”.

Kafin cimma wannan manufa, majalisun dokokin jihohin 7 na da gagarumar rawar takawa. Hon Aminu Giɗaɗo shugaban kwamitin kula da harkokin muhalli da sauyin yanayi a majalisar dokoki ta jihar Sokkwato ya fayyace hanyar da za su bi, “Ta hanyar yarda ko amincewa da kasafin daya shafi ayyuka raya muhalli da kuma magance matsalolin da sauyin yanayi kan zuwa da su a kowane lokaci”.

Dama dai manzarta sun daɗe suna bayyana alfanun samar da tsare tsare na bai daya a tsakanin gwamnatocin arewa domin mangance ƙalubalen da yankin ke fuskanta a fannoni daban daban.

Leave a Reply