Sojin Isra’ila sun gabatar da shirin kwashe mutane yayin da Netanyahu ya sha alwashin mamaye Rafah

0
95

Sojojin Isra’ila sun gabatar da wani shiri na “kwashe” fararen hula daga Gaza, bayan da Firaiminista Benjamin Netanyahu ya ce kai farmaki ta ƙasa kan birnin Rafah na kudancin Falasdinawa ya zama wajibi domin samun nasara baki ɗaya.

Gwamnatocin ƙasashen waje da ƙungiyoyin agaji sun sha bayyana fargabar cewa irin wannan farmakin zai janyo asarar rayukan fararen hula a Rafah, inda Falasdinawa kusan miliyan 1.4 — galibinsu da suka yi gudun hijira daga wasu yankuna — suke samun mafaka a can.

Har ila yau, ita ce hanyar shigar da agajin da ake tsananin buƙata, inda ake shigar da kayayyakin daga maƙwabciyarta Masar.

Sojojin Isra’ila “sun gabatar wa da majalisar ministocin yaƙin wani shiri na kwashe jama’a daga yankunan da ake gwabzawa a Gaza, da kuma shirin gudanar da aikin ƙaddamar da hare-hare da ke tafe”, a wata sanarwa da ta fito daga ofishin Netayahu a cikin harshen Hebrew a yau Litinin.

KU KUMA KARANTA: Wani mutum ya cinna wa kansa wuta a wajen ofishin jakadancin Isra’ila na Amurka

Sanarwar ba ta bayar da cikakken bayani kan yadda za a kwashe fararen hular ko kuma inda za a kai su ba.

Sanarwar ta zo ne bayan da ƙwararru da Masar, Qatar da Amurka suka gana a birnin Doha, taron da ya kuma samu halartar wakilan Isra’ila da na Hamas, kamar yadda kafar yada labarai ta Masar mai alaƙa da gwamnatin Masar ta bayyana, wanda shi ne yunƙuri na baya-bayan nan da aka yi na ganin an cimma matsaya kafin watan Ramadan mai alfarma.

Leave a Reply