Kotunan da mu ke da su a Najeriya sun wadata wajen shari’un cin-hanci – Shugaban ICPC

0
72

Shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci ta ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu ya ce ba lalle sai an kafa kotuna na musamman ba don sauraron shari’un cin-hanci da rashawa.

Dakta Aliyu ya faɗi hakan yayin da ya ke magana a taron manema labarai a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairun da mu ke ciki, a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Hakan ya yi hannun riga da matsayar magabata a yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya.

“Ba sai an ƙirƙiro kotuna na musamman ne za a iya gudanar da shari’un waɗanda ake tuhuma da almundahana ba, don waɗanda a ke da su sun wadatar”, a cewar Dakta Aliyu.

Dakta Aliyu daga jihar Jigawa, wanda kusan shi ne mafi ƙarancin shekaru da ya zama shugaban ICPC, ya ce don cimma nasarar shari’un ma zai riƙa zuwa kotu da kansa.

Ra’ayin Dakta Aliyu ya sha bambam da na masu sharhi da ma tsoffin masu ruwa da tsaki na hukumomin yaƙi da cin hanci da ke ganin akwai buƙatar kafa kotunan yaƙi da cin hanci, don ta hakan ne kawai za a iya samun nasarar yaƙi da masu karkatar da dukiyar jama’a.

Ga matsayar tsohon kakakin hukumar EFCC, Dakta Othman Abubakar “cin hanci da rashawa laifi ne wanda sai kotun musamman ta saurara.

KU KUMA KARANTA:Mayar wa Sarakunan gargajiya waɗansu ikon su, na ɗaya daga cikin hanyoyin da za’a samu nasarar yaƙi da matsalolin tsaro

“Kotun musamman ɗin ba wai cewa mala’iku ne za su zo su zauna a kotun ba, a’a, lauyoyin dai da mutane masu basira su suke haɗawa a yi irin waɗannan (tribunal) amma a yanda a ke tafiya a kotunan Najeriya abun ɓacin rai, ba za a je ko ina ba.”

In za a tuna, tsohuwar Shugabar EFCC, Hajiya Farida Waziri ta ce ba ma batun kotuna ba ne kawai, akwai buƙatar gwajin ƙwaƙwalwar ɓarayin biro.

Sabon Shugaban na ICPC wanda ya yi alwashin yin aiki tare da sauran hukumomin yaƙin, ya ba da tabbacin samar da sauyin da jama’a za su shaida haƙiƙanin yaƙin.

Najeriya na da hukumomin yaƙi da cin hanci da sun kusan yatsun hannu kamar EFCC, ICPC, Kotun Ɗa’ar Ma’aikata, Kwamitocin Shari’a amma sai a wayi gari a na zargin babban jami’in gwamnati da wawure biliyoyi ko ma tiriliyoyin Naira.

Leave a Reply