An kashe fiye da mutum 60 a rikicin ƙabilancin ƙasar Papua, New Guinea

0
171

Ƴan sanda sun sun ce an gano gawawwaki 64 da aka yi musu jina-jina zube a kan wata hanya a wani yanki yanki mai nisa a Papua New Guinea, abin da ke nuna cewa ƴaƙin da aka jima ana yi tsakanin ƙabilun yankin na ƙara ƙazancewa.

An yi amanna cewa, mutanen da aka kashe mayaƙan wata ƙabila ne, da mayaƙan wata ƙabilar daban suka yi wa kwanton ɓauna ranar Lahadi.

Lamarin ya faru ne a kusa da garin Wabag, kimanin kilomita 600 arewa maso yammacin babban birinn ƙsar Port Moresby.

Kwamishinan ƴan sanda David Manning Monday ya bayyana lamarin a matsayin wani “gagarumin dabbanci”, sannan ya bayyana cewa ana shirin gudanar da wani “aiki na musamman” a yankin, don “mai da doka da oda.”

“An bai wa waɗannan jami’an umarni a fayyace cewa su yi amfani da kowane irin ƙarfi da ake buƙata don hana sake faruwar irin wannan tashin hankalin, yana mai cewa, “Wannan ya haɗa da amfani da ƙarfi fiye da ƙima idan aka yi wa rayuwar jami’an tsaro da ta fararen hula barazana.”

KU KUMA KARANTA: Afirka ta Kudu za ta tura dakaru 2,900 don yaƙi da ƴan bindiga a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

Yankin wanda ke fama da tashin hankali tsawon shekaru, ya zama wani wajen ramuwar gayyar kashe-kashe tsakanin ƙabilun Sikin, da Ambulin da wasu ƙabilun.

Wasu hotuna masu tada hankali da ƴan sanda suka fitar daga wajen da lamarin ya faru, sun nuna gawawwaki jina-jina kwance a gefen titi, sannan an loda wasu a bayan wata motar ɗaukan kaya.

Wasu mutanen an cire musu wasu gaɓoɓi, sannan wasu ba kaya a jikinsu, yayin da aka ɗaura musu kwalabe ko gwangwanaye a ƙirjinsu.

A ranar Litinin, ƴan sanda sun ce an ringa jin ƙarin bindiga a wani waje kusa da inda lamarin ya faru, kuma an ci gaba da gano wasu gawawwakin daga dazukan da ke kusa da hanyar.

“Mun yi amanna cewa akwai wasu gawawwakin a cikin daji, a cewar mataumakin kwamishinan ƴan sanda Samson Kua.

An shafe ɗaruruwan shekaru ƙabilu na faɗa da juna a yankin na Papua New Guinea, amma ƙaruwar sojojin haya da bazuwar makamai masu sarrafa kansu, sun sa faɗace-faɗacen sun ƙara ƙazancewa, sannan an ƙara samun yaɗuwar tashin hankalin cikin gaggawa.

Kua ya ce ƴan bindigar na amfani da muggan makamai, da suka hadar da bindigogi samfurin SLR, da AK-47, da M4, da AR15 da kuma M16, sai kuma bindigar harba-ruga da bindigogin da ake ƙerawa a gida.

Muƙaddashin kwamandan ƴan sandan yankin, Patrick Peka yace da dama daga waɗanda aka kashe ɗin sojojin haya ne – waɗanda suke yawo a yankin suna tayin taimakawa ƙabilu taimaka musu wajen ɗaukan fansa a kan abokan gabarsu.

“Ƴan sanda da gwamnati ba za su iya yin wani abin a-zo a-gani ba lokacin da shugabanni da masu faɗa-a-ji suke safarar makamai, sannan suke daukan sojojin haya daga wasu sassan yankin,” a cewar Peke.

Gwamnatin Papua New Guinea ta yi kokarin daƙile rikicin, da shiga tsakani, da yin afuwa da ma wasu matakan don taƙaita yaɗuwar rikicin, sai dai babu wata nasarar a zo a gani.

Rundanar soja ta tura fiye da sojiji 100 yankin, sai dai tasirinsu taƙaitacce ne, sannan mayaƙan ƙabilu sun fi jami’an tsaro yawa sun fi su makamai.

A mai yawan lokuta, an fi samu kashe-kashe ne a yankuna masu nisa, inda ake kai farmaki da kwanton ɓauna a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da aka kai a baya.

A baya an sha kai farmaki kan fararen hula da suka haɗa da mata masu ciki da ƙananan yara.

Leave a Reply