Mutane 53 sun mutu a wani rikicin ƙabilanci a ƙasar Guinea

‘Yan sandan Papua New Guinea sun ce mutane 53 ne aka kashe a wani rikicin ƙabilanci a yankin tsaunukan ƙasar da ke fama da rikice-rikice, wannan shi ne kisan kiyashi na baya-baya da aka gani mai alaƙa da daɗaɗɗiyar taƙaddama a yankin.

Kwamishinan ‘yan sandan ƙasar David Manning a ranar Lahadi ya ce jami’ai da sojoji sun kwaso gawarwakin maza 53.

Ana kyautata zaton an kashe su ne a kusa da garin Wabag, mai tazarar kilomita 600 daga arewa maso yammacin Port Moresby babban birnin ƙasar.

KU KUMA KARANTA:Najeriya na fuskantar matsalar tattalin arziƙi

Nan take dai ba a bayyana takamaimai yadda kisan ya faru ba, amma ‘yan sanda sun ce an sami rahoton zafafan harbe-harbe a yankin.

Ana kyautata zaton lamarin na da nasaba da rikicin da ke faruwa tsakanin ‘yan ƙabilar Sikin da Kaekin.

Ƙabilun yankin sun shafe shekaru aru-aru suna faɗa da juna a Papua New Guinea, amma kwararar makamai masu sarrafa kansu sun sa faɗan zama da muni.

‘Yan sanda sun samu bidiyo da hotuna da aka ce daga wurin da lamarin ya faru suka fito. Hotunan sun nuna gawarwaki jina-jina kwance a gefen titi, wasu kuma jibge a bayan wata babbar motar dakon kaya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *