An saki Murja Kunya daga gidan gyaran hali

0
137

Gidan gyaran hali na Nijeriya reshen Jihar Kano ya tabbatar da cewa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya saki Murja Ibrahim Kunya daga gidan bayan samun takardar daga kotu.

Mai magana da yawun gidan gyaran halin SC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa sai da suka samu takarda daga kotu tukuna suka sake ta.

SC Musbahu ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa wadda ke cewa Murja Ibrahim Kunya ta tsere daga gidan yari.

“Gidan ajiya da gyaran hali gida ne wanda takarda ce take kawo mutum, hakazalika takarda ce take fitar da mutum, duk mutumin da aka kawo shi gidan ajiya da gyaran hali matuƙar takardarsa ba ta cika ba ko aka samu kuskure a ciki to ba za a sake shi ba,” in ji SC Musbahu.

KU KUMA KARANTA: Murja Kunya ba ta gudu daga gidan gyaran hali ba – Kakakin gidan gyaran hali

Ya bayyana cewa gidan gyaran hali kamar banki yake, sai takardu sun cika an tabbatar babu kuskure kafin ake iya karɓar.

A makon da ya gabata ne Hukumar Hisbah a Kano ta kama Murja Ibrahim Kunya inda har ta gurfanar da ita a gaban kotu bisa wasu zarge-zarge da suka haɗa da yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta.

Bayan gurfanar da ita ne a gaban kotu aka tura ta gidan gyaran halin da ke jihar ta Kano.

Leave a Reply