An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga ‘Mai Dubu-Dubu’ a Sakkwato

’Yan sanda sun aika ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Hantsi, wanda aka fi sani da Mai Dubu-Dubu, lahira a Jihar Sakkwato.

Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i, ya ce jami’an rundunar sun ƙwato makamai daga Mai Dubu-Dubu bayan da suka aika shi barzahu a Ƙaramar Hukumar Kware.

Sanarwar da ya fitar ta ambato kwamishinan rundunar, Ali Hayatu Kaigama, yana cewa Mai Dubu-Dubu da aka kashe a kauyen Tungar Rana yana daga cikin dillalan makamai da ke sayar wa sauran ’yan bindiga.

“Da misalin karfe 0330 na dare Babban DPO na yankin Kware da jami’ansa suka je farautar Mai Dubu-Dubu a wani daji bayan sun ga alamar motsinsa.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 254 a cikin mako guda

“Ko da ɗan bindigar ya gan su, sai ya fara harbi yana ƙoƙarin tserewa, amma ba tare da ɓata lokaci ba jami’anmu suka harbe shi har lahira, sauran abokansa kuma suka tsere da raunin harbi a jikinsu.

“Mun ɗauko gawarsa kuma a wajen da muka kashe shi mun samu bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da harsasai 21,” in ji sanarwar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *