Murja Kunya ba ta gudu daga gidan gyaran hali ba – Kakakin gidan gyaran hali

Daga Ibraheem El-Tafseer

A safiyar yau Lahadi ne, ake ta raɗe-raɗin cewa fitacciyar ‘yar Tiktok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya ta yi ɓatan dabo daga gidan gyaran hali a Kano. Jama’a sun cika da mamaki ganin cewa ta yaya za’a ce an neme ta an rasa. Sai dai idan an sake ta ne da gangan.

Maganganu da dama suna ta fitowa daga bakin jama’a. Sai dai Kakakin gidan gyaran halin, ya shaida wa manema labarai cewa “tun ranar Alhamis mu ka saki Murja bisa umarnin kotu’

Kakakin gidan gyaran hali na jihar Kano AC Misbahu Kofar Nassarawa ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewa sananniyar ‘yar Tiktok Murja Kunya ba guduwa ta yi daga gidan gyaran hali ba.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta aike da Murja Kunya gidan gyaran hali a Kano

A cewar sa, tun ranar Alhamis takarda ta zo daga kotu don neman a sake ta, kuma gidan yarin ya sake ta a ranar.

Ya ƙara da cewa kotu ce ta kawo ta ajiya a wajensu, kuma kotu ce ta ce su sake ta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *