Connect with us

Labarai

An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi wajen cire dala 6.2m daga CBN — Boss Mustapha

Published

on

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya musanta ba da izinin biyan Dala miliyan 6.2 ga masu sanya ido kan harkokin zaɓe na ketare.

Boss Mustapha ya bayyana hakan ne a gaban wata babbar kotu da ke Abuja a inda ya shaida mata cewa, ba shi da masaniya kan wata takardar ba da izini ga tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, wadda ake zargin ta sahale masa biyan sama da Dalar Amurka miliyan 6.2 ga masu sanya ido a zaɓe na ƙasashen waje.

Tsohon Sakataren Gwamnatin wanda yana daga cikin shaidu a ƙarar da ake tuhumar Emefiele ya ce, a tsawon shekara biyar da wata bakwai da ya yi yana riƙe da wannan muƙamin, ba shi da masaniya kan takardar.

KU KUMA KARANTA: Bamu da wani Farfesan bogi a Jami’ar Bayero – Shugaban Jami’ar

Boss Mustapha ya kuma bayyana wa kotun cewa, ba daga ofishinsa takardar ta fito ba kuma ba daga fadar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari takardar biyan kuɗaɗen ta fito ba.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ya kuma shaida wa kotun cewa, babu ruwan Gwamnatin Tarayyar da biyan masu sa-ido na ƙasashen wajen kuɗaɗe.

A ƙunshin takardun bayanan da jagoran lauyoyin masu ƙara, Rotimi Oyedepo suka gabatar masa, tsohon Sakataren Gwamnatin ya ce, bai taba ganin su ba, hasali ma sa hannun da suke ɗauke da su na Buhari na jabu ne, sai dai ya bar wa kwararru hakan su tabbatar.

Mista Emefiele dai na fuskantar tuhume-tuhume 20 a shari’ar, waɗanda suka haɗa da cin hanci da rashawa, haɗa baki domin aikata laifi, da cin amana da ungulu da kan zabo da kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka $6,230,000.

Ana zargin tsohon Gwamnan na CBN da yin amfani da sa hannu na jabu domin karɓar kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba.

Masu sa-ido a babban zaɓen ƙasar da aka yi a 2023 na ƙasashen waje ake ikirarin an biyan kuɗaɗen.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like