Kotu ta aike da Murja Kunya gidan gyaran hali a Kano

0
300

Hukumar Hisba ta gurfanar da shahararriyar yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya gaban kotun shari’ar addini musulinci dake zaman ta a unguwar Gama PRP Kano, bisa zarginta da aikata laifukan kawo ɓata-gari cikin dare da aikata baɗala, tada hatsaniya da kuma razanarwa wanda yin hakan ya saba da sashi na 341, 275 da 227 na kundin SPCL.

Hukumar Hisbah ta cafke ta tare da gurfanar da ita a gaban kotun, bayan ta karɓi ƙorafe-ƙorafen mazauna unguwar Tishama a ƙaramar hukumar Nasarawa dake Kano.

Bayan gurfanar da ita a gaban kotun an karonta mata ƙunshin zargin, inda ta musanta dukkan tuhumar da ake yi mata.

Lauyan dake kare wadda ake tuhumar Barista Aliyu Umar  ya roƙi kotun ta bayar da belin ta, dogaro sashi 35 da 36 na dokokin kasa da kuma sashi na 168, 172 da 173 na kundin SPCL.

KU KUMA KARANTA: Hisbah ta cafke Murja Ibrahim Kunya a Kano

Lauyan gwamnatin jihar Kano da ya wakilci kwamishinan shari’a na jahar Kano, Barista Aminu Umar bai yi suka akan rokon wadda ake tuhumar ba.

‘’Ba mu da suka akan wannan roko domin bayar da beli hurimin kotu ne’’ lauyan Gwamnatin Kano’’.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed ya bayar da umarnin ci gaba da tsare wadda ake zargin a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 22 ga watan fabarairun 2024.

Leave a Reply