Masu tsatsauran ra’ayin Isra’ila sun yi yunƙurin daƙile wani ɗan jarida na kafar watsa labarai ta TRT sashen Larabci a Tel Aviv daga ɗaukar rahoto dangane da zanga-zangar da ake gudanarwa dangane da ƙin jinin gwamnatin Isra’ila da buƙatar tsagaita wuta da musayar fursunoni.
Masu zanga-zanga ƴan Isra’la da kuma iyalan waɗanda ake riƙe da su a Gaza sun rufe babbar hanyar Tel Aviv a ranar Asabar inda suke ta zanga-zanga dangane da gwamnatin Firaiminista Benjamin Netanyahu mai tsatsauran ra’ayi dangane da watsi da buƙatar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni a Gaza.
Bayan harin da Yahudawa masu tsatsauran ra’ayi suka kai wanda ya kawo cikas ga ɗaukar rahoton, wakilin TRT na sashen Larabci Fehmi Shtewe ya wallafa labari a shafinsa na X inda yake cewa, “Har wa yau, ƴan Isra’ila sun ƙara kai mana hari, a wannan karon daga tsakiyar Tel viv, inda suka yi yunƙurin hana mu kawo rahoto dangane da zanga-zangar da fusatattun ƴan Isra’ila ke yi dangane da yaƙin Gaza da kuma gaza samun nasarar a yaƙi bayan kwanaki 127! Za mu ci gaba da kawo rahoto na gaskiya!”
KU KUMA KARANTA: Isra’ila na tsoro kada Amurka ta amince da ƙasar Falasɗinu
Ba wannan ne karo na farko ba da masu tsatsauran ra’ayin Isra’ila ko sojojin Isra’ila suke kai hari kan wakilan sashen Larabci na TRT ba.
Ko a watan Oktoban da ya gabata sai da sojojin na Isra’ila suka kai hari ga ƴan jaridar TRT kan iyakar Lebanon da Isra’ila a lokacin da suke ƙoƙarin kawo rahoto dangane da rikicin Hamas da Isra’ila.