Al’umma sun fita zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihar Neja

0
116

Daga Ibraheem El-Tafseer

A yau Litinin da hantsi ne, ɗaruruwan al’umma a Minna da ke jihar Neja a Najeriya suka fito zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake fama da shi a ƙasar.

Masu zanga-zangar sun haɗa da mata da matasa inda suke rera waƙoƙii yayin da jami’an tsaro har da ‘yan sanda ke gefe suna kallo.

Wasu mazauna birnin da suka tattauna da BBC sun ce tsadar kayan masarufi da rashin taɓuka abin a zo a gani daga ɓangaren gwamnati wajen samar da sauƙi a lamarin ne ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukansu.

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ta ɓarke a Senegal bayan sanar da ɗage zaɓe

Mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba a lokacin da yake yi wa masu zanga-zangar jawabi, ya ce gwamnati tana sane da irin ƙunci da wahalar da jama’a suke fuskanta a yanzu.

Ya ce gwamnati tana aiki domin rage halin matsi da aka shiga da kuma tasirin da ake gani sanadin cire tallafin mai.

Leave a Reply