An yi jana’izar tsohon gwamnan jihar Yobe a ƙasar Saudiyya (Bidiyo)

0
152

Daga Ibraheem El-Tafseer

A safiyar yau Litinin ne aka yi jana’izar tsohon gwamnan jihar Yobe Sanata Bukar Abba Ibrahim a ƙasar Saudiyya. Daman ya je jinya ne a can sai ajali ya cimmasa.

Sanata Bukar ya yi gwamnan jihar Yobe har sau uku, sannan ya yi Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas sau uku. Sannan ya yi Kwamishina tun ana haɗe Yobe da Borno.

Rasuwar Bukar Abba ta jijjiga al’ummar jihar Yobe, kasantuwar yadda ya gudanar da mulkinsa cikin kwanciyar hankali da ƙaunar duk ɗan jihar ba tare da nuna bambancin yare ko yanki ba.

KU KUMA KARANTA: Tsohon gwamnan Yobe, Bukar Abba Ibrahim, ya rasu

Bukar Abba ya kawo ci gaba ta fannoni da dama a jihar Yobe, ya sama wa mutane da yawa aiki a lokacinsa. Ya rasu yana da shekaru 75, ya bar mata biyu da ‘ya’ya 17.

Yanzu haka gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ne yake karɓar ta’aziyyar rasuwar sa a babban masallacin juma’a na jihar Yobe da ke birnin Damaturu.

Kalli bidiyon jana’izar a nan:

Leave a Reply