EFCC ta kama tsohon minista bisa laifin zamba

0
135

Jami’an hukumar shiyyar Legas na hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, sun cafke tsohon ministan kasuwanci da masana’antu, Charles Chukwuemeka Ugwuh, bisa zarginsa da haɗa baki da kuma zamba har N3.6bn.

An kama Ugwuh ne tare da Cif Geoffrey Ekenma a ranar 11 ga Janairu, 2024 a No.2, Musa Yar Adua way, New Owerri, Jihar Imo, bayan wata takardar koke ga hukumar daga wani bankin zamani kan zamba da ake zargin wani kamfani, Ebony Agro. Industries Ltd., mai alaƙa da tsohon Ministan.

Bincike ya nuna cewa Ugwuh da Ekenma, Manajan Darakta na Ebony Agro Industries Ltd., ana zargin sun samu lamuni daga bankin domin saye da samar da shinkafa.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta sake buɗe shari’ar zargin ɓatan N772bn akan Kwankwaso, Fayose da wasu tsofaffin gwamnoni 11

Sai dai wanda ake zargin, a cewar mai shigar da kara, ya kasa cika hakkinsa na bankin, kuma duk ƙoƙarin da ya yi na ganin ya biya bashin kuɗin ya ci tura.

Za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply