Ko Ojukwu bai ci amanar Najeriya irin yadda Buhari ya ci ba – Bello Yabo

0
125

A wani faifan bidiyo da ya bayyana an ji yadda Shararren Malamin addinin musulunci, Bello Yabo ya yi wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari Raddi game da irin yadda aka yi facaka da kuɗi a zamanin mulkin sa.

Malamin acewar sa an yi shagali an yi facaka da kuɗi fiye da zato.

Ga abinda ya ce: ”kwanaki na shiga kasuwa sai wani ke tseguntamin cewar ”waɗannan jiragen fa daka gani na mai saida katin can ne”,Na ce a’a wannan lamari ba gaskiya ba, ya sake cemin wallahi na shi ne ai shi wannan ɗin da kake gani hoto ne,yaushe za a ce mai saida kati ne zai mallaki jiragen sama.”

KU KUMA KARANTA: Mahadi Shehu ya chaccaki tsohon shugaban Najeriya, Buhari

Malamin ya cigaba da cewa ”Duk wannan wadaƙar fa a zamanin Buhari aka yi su saboda haka, har Buhari ya kamata shima a kama shi saboda yadda ya ci amanar ƙasa, wallahi irin yadda Buhari yaci amanar ƙasa ko Ojukwu bai yi haka ba.

Malamin ya ce ko Ojukwu da ya sabautar da yaƙin basasa bai ci amanar ƙasar nan irin yadda Buhari ya ci ba.

Leave a Reply