Za mu ƙara albashin kowani ma’aikaci a Najeriya – Shugaba Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce za a yi wa ma’aikatan Najeriya ƙarin albashi a wannan shekarar ta 2024.

Shugaban ya ƙara da cewa “za mu ƙara albashin kowanne ma’aikaci a Najeriya, domin ƙarin shi ne abu mafi dacewa”

Dole ne mu tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya. Da yake jawabin sabuwar shekara a jihar Legas shugaba Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da an samar da ababen more rayuwa da kuma inganta tattalin arzikin ƙasar da zai kawo sauƙaƙa rayuwar ma’aikata da ‘yan Najeriya.

“Gwamnatinmu za ta yi aiki tuƙuru domin tabbatar da mun taɓa rayuwar kowanne ɗan Najeriya” inji shi.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya dawo da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu

Tinubu ya ce “Zuwa yanzu muna dab da kammala shirye-shiryen da muka kwashe watanni 7 da suka gabata na farfaɗo da tattalin arziki, domin samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya baki ɗaya.

Shugaba Tinubu ya kuma yi tsokaci kan irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen ganin an inganta ɓangaren samar da wutar lantarki, duba cewa ba za a iya samun ci gaban da ake da buƙata ba, ba tare da wutar lantarki ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *