Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

Aƙalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a ranar Asabar a wani hatsarin mota a garin Kwanar Gujungu da ke ƙaramar hukumar Taura na jihar Jigawa.

Alfijir labarai ta rawaito mai magana da yawun ƴan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse, a ranar Lahadi.

Shiisu ya ce hatsarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 12:00 na rana, inda motoci biyu, ƙirar Honda saloon mai lamba NSR 469 AE, da wata motar Golf mai lamba AUY 292 XA suka yi karo da juna.

Ya ce motar Honda na ɗauke da fasinjoji biyar, sai direbanta mai suna Abdullahi Muhammad, yayin da motar Golf kuma ke ɗauke da fasinjoji huɗu, da direban Safiyanu Mamu.

KU KUMA KARANTA: Mutum 16 sun mutu, 30 sun jikkata a hatsarin tirela a Jos

Ya ce tawagar ma’aikatan hedikwatar ‘yan sanda ta Taura sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai waɗanda abin ya shafa zuwa babban asibitin garin Taura, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ahmadu Abdullahi, a madadin sauran jami’an rundunar, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu tare da addu’ar Allah ya gafarta musu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *