An kashe mutum 16 a wani hari a Jihar Filato

Aƙalla mutum 16 ne suka mutu a wani hari da aka kai ƙauyen Mushu da ke Jihar Filato a yankin arewa ta tsakiyar Najeriya.

Kamfanin dilancin labarai na AFP wanda ya ce rundunar sojin ƙasar ce ta tabbatar masa da harin, ya rawaito Kyaftin Oya James ya shaida mata cewa lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Asabar.

Rikicin ƙabilanci da kuma na manoma da makiyaya ya zama tamkar ruwan dare a Jihar Filato, wanda aka shafe shekaru ana fama da shi, kuma yana yawan jawo asarar rayuka.

“Muna barci sai kwatsam muka ji wata ƙara mai ƙarfi,” in ji wani mazaunin ƙauyen Markus Amorudu.

“Mun tsorata sosai saboda ba mu tsammaci wani hari ba. Mutane sun ɓuya, amma maharan sun kama da yawa daga cikinmu, an kashe wasu an jikkata wasu,” a cewar ganau ɗin.

Har yanzu ba a gano musabbin kai harin ba, sannan ba a san waɗanda suka kai shi ba.

KU KUMA KARANTA: Za mu hukunta masu hannu a harin Tudun Biri — Hafsan Tsaro

Sai dai tuni aka aika jami’an tsaro don kare ɓarkewar rikici a yankin, inda ake yawan samun hatsaniya tsakanin makiyaya da yawancinsu Musulmai ne da kuma manoma da yawancinsu Kiristoci ne.

Gwaman Jihar Caleb Mutfwang ya yi Allah wadai da wannan hari yana mai ƙiransa “mummunan da bai kamata ba,” tare da shan alwashin gano waɗanda suka kai shi da kuma tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci.

“Gwamnati za kuma ta ɗauki matakan da suka dace don daƙile hare-haren da ake kai wa kan fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba,” kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Gyang Bere ya gaya wa manema labarai.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *