Tsoffin takalman Sarkin Masar Tutankhamun wadda suka yi shekaru 3,300

0
272

Waɗannan takalma dai, an samo su ne a cikin kabarin Sarkin (Tutankhamun) wadda ya yi mulki daga shekara ta 1336 zuwa 1327 kafin haihuwar Annabi Isah AS, a ƙarƙashin Daula ta 18.

Tutankhamun tsohon sarki (Fir’auna) ne na Masar, wadda a cikin tarihin sabuwar Masarautar Masar shi ne na ƙarshe a cikin zuri’arsa da ya yi mulki a ƙarshen daular 18.

An yi imanin cewa mahaifinsa shi ne Sarki Akhenaten, wadda aka samu burbushin sassan jikinsa a cikin kabarin KV55 da masana kimiyyar ƙarƙashin ƙasa suka gudanar da bincike. A Afirka ta da, Sarki Tutankhamun ya na ɗaya daga cikin manyan sarakuna.

Har ila yau, su dai waɗannan takalma na alfarma su na a killace a gidan adana kayan tarihi na birnin Alƙahira, da ke Masar.

Bugu da ƙari, takalman an yi su ne da sassaƙen itace kuma aka shimfiɗe su da Fata, sannan aka yi masu ado da Zinariya.

Haka nan, akwai zanen siffofi biyu na mutane shimfiɗe a tafin kowane ɓarin takalmi; Wadda hakan ke nuni da al’ummar Nubian (ko Afirka ta kudu da hamadar Sahara) da fursunoni na Asiya.

KU KUMA KARANTA: Tarihin marubuci Abubakar Imam (2)

Har wa yau, a ƙarƙashin yatsun ƙafafu na kowane ɓarin takalmi akwai wasu zane guda huɗu, haka ma daga ƙarƙashin diddige, wadda ke nuni da mubaya’a. Akwai kuma maɗauri wadda shi ma ke nufin risinawa ga Sarki.

Masarawa na zamani har yanzu su na nufin sanya zanen abokan gaba a ƙarƙashin takalmansu ko ƙarƙashin ƙafafunsu, a matsayin alamar raini ko ƙasƙanci.

Binciken, wadda aka buga a cikin littafin, “Tutankhamun’s Footwear: Studies of Ancient Egypt Footwear,” shi ne cikakken bincike na farko na takalman shekaru 3,300 tun lokacin da Howard Carter ya gano da kabari na Sarki Tutankhamun a 1922.

Binciken da Howard Carter ya yi na kabarin Tutankhamun a shekara ta 1922, na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da aka gano a tarihi. An ɗauki shekaru 10 kafin Carter da tawagarsa su kammala binciken kayan tarihi na kabarin sun kuma gano ababe da dama, takalmin na daga ciki.

A karon farko tun lokacin da aka gano takalman, an yi nazari dalla-dalla ta hanyar amfani da bayanan Carter da kyakkyawan hoto na Harry Burton tare da nazarin mawallafin na kayan tarihi, duk an ajiye su a cikin gidan adana kayan tarihi na Masar da ke Alƙahira da Luxor.

Leave a Reply