Jabun kuɗaɗe sun bazu a gari — CBN

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ja hankalin ’yan Najeriya kan jabun takardun kuɗin ƙasar da ke yawo a cikin al’umma a sakamakon raɗe-raɗin da ake yaɗawa na ƙarancin tsabar kuɗi.

Kakakin CBN, Hakama Sidi Ali ta shawarci al’umma da su kasance masu lura ganin cewa masu jabun kuɗaɗe na amfani da su a matsayin kuɗin mota ko a wurin yin cefane da gidajen abinci sauransu.

Sanarwar ta CBN ta ce “Dokar CBN ta tanadi hukucin ɗaurin aƙalla shekaru biyar ga duk wanda ya buga jabun kuɗaɗe.

“CBN na aiki da hukumomin tsaro da na hada-hadar kuɗaɗe wajen ganowa da ƙwace jabun kuɗaɗe da kuma tsare masu buga su.” in ji jami’ar.

Daga nan sai ta umarci bankuna, ’yan canji da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe da su ɗauki matakan da suka dace wajen ganowa da kuma hana yaɗuwar jabun kuɗaɗe.

Ta ƙara da cewa, “ana ƙira ga jama’a su kai ƙarar duk wanda suka ga yana yin jabun kuɗaɗe ga ofishin yan sanda ko na CBN mafi kusa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *