CBN zai rufe asusun bankin da ba su da BVN

0
122

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar cewa zai rufe asusun bankin duk waɗanda ba su da lambar BVN ko NIN. 

CBN ya cewa daga watan Afrilun 2024, duk asusun bankin da ba a haɗa da lambar BVN ko NIN ba, za su daina aiki.

Babban bankin ya umarci duk masu asusun banki da na e-wallet da su tabbata sun haɗa su da NIN ko BVN ɗinsu kafin 31 ga watan Janairu, 2024.

Sanarwar da CBN ya fitar ɗauke da sa hannun daraktan kuɗaɗe da na tsare-tsare, Chibuzo Efobi da Haruna Mustapha, ta ce daga watan Afrilun 2024, “za a haramta sanya kuɗi ko cirewa daga asusun banki marasa BVN ko NIN.”

KU KUMA KARANTA: Babu ranar daina amfani da tsofaffin kuɗi — CBN

BVN shi ne lambar tantance masu ajiyar banki wanda CBN ya ɓullo da shi, wanda kowane mutum aka haɗe duk asusunsa na banki da BVN ɗaya.

NIN kuma ita ce lambar shaidar ɗan ƙasa, wanda a watannin baya Gwamnatin Tarayya ta wajabta wa kowa haɗe nasa da lambobin wayarsa.

Leave a Reply