Isra’ila da Hamas sun amince a kara wa’adin tsagaita wuta da kwanaki bakwai

0
146

Isra’ila da ƙungiyar Hamas mai rajin kare hakkin Falasɗinawa sun amince su tsawaita yarjejeiyar tsagaita zuwa karin kwana bakwai.

Kazalika sojojin Isra’ila sun ce za a ci gaba da mutunta yarjejeniyar “bisa ƙoƙarin masu shiga tsakani na ci gaba da ganin an saki ƙarin mutanen da aka yi garkuwa da su, kuma a kan sharuɗan da aka yarda da su.”

Ƙasar Qatar wadda ke shiga tsakani ta tabbatar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince su tsawaita tsawaita wa’adin yarjejeniyar, wanda zai kare ranar Alhamis mai zuwa da safe.

Leave a Reply